A cewar rahotannin da wakilan Kamfanin Dillancin Labaran Hauza suka aiko mana, waɗannan taruka sun ƙunshi darussa na basira, ilimi, da al'adu, wanda ke nuna yadda saƙon gaskiya na Musulunci yake ci gaba a nahiyar Afirka.
Natsuwa Da Haɗin Kai A Jihar Katsina
A garuruwan Mashi da Muduru da ke Jihar Katsina, an gudanar da zaman juyayin rana ta uku cikin kwanciyar hankali. A garin Mashi, zaman ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Malam Abdulkareem Ibraheem, inda aka yi bayani kan darussan Waki'ar Karbala da kuma muhimmancin kiyaye koyarwar Imam Husain (AS). Haka kuma, a garin Muduru, an gudanar da zaman ne a Muhallin Fudiyya ƙarƙashin jagorancin Malam Sadisu Abdullahi Muduru, inda aka jaddada irin sadaukarwar da aka yi domin kare addinin Musulunci.
Bayani Kan Alaƙar Ashura Da Intizar, Da Kaddamar Da Littafin Jagora A Kano
Masallacin Juma’a na Fagge da ke birnin Kano ya karɓi baƙuncin dubun-dubatar masoya Ahlul Baiti. Bayan kammala waƙoƙin juyayi da Malam Shamsu Fudiyya ya jagoranta, Shaikh Tijjani Ahmad ya gabatar da jawabi mai taken "Alaƙar Ashura da Intizar". A cikin jawabin nasa, ya ƙaryata fahimtar da ke cewa jiran bayyanar Imam Mahdi (AF) na nufin zaman banza ko yawaita fasadi, yana mai jaddada cewa ainihin intizar yana nufin gyara kai, tsayuwa kan gaskiya, da tabbatar da adalci.
Bayan haka, an ƙaddamar da littafin rayuwar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, mai taken "Mai Haƙuri na Tare da Nasara", inda matasa da sauran mabiya gwagwarmaya suka nuna sha'awarsu ta mallakar littafin domin amfana da darussan da ke ciki.
Labarin Jarumtar Kiristan Da Ya Yi Shahada A Karbala A Garin Funtua
A garin Funtua kuwa, Malam Ashiru Abdullahi ya mayar da hankali kan yadda saƙon Imam Husain (AS) ya tsallake iyakokin addini. Ya kawo labarin tarihi na wani Kirista (kamar yadda aka sani na Wahab Nusrani ko Jon) wanda ya gane gaskiya har ya bi sahun Imam Husain (AS) kuma ya yi shahada a Karbala. Malamin ya yabi irin jarumtar mahaifiyar shahidin wajen ƙin karɓar diyya ta duniya, yana mai jaddada cewa tafiyar Imam Husain hanya ce ta rayuwa wacce ke koyar da basira da neman hasken imani daga Allah Madaukakin Sarki.
Sauraron Jawabin Sayyid Zakzaky Da Shirye-Shiryen Ranar Jarirai A Suleja
A garin Suleja, bayan gabatar da zikirar waƙoƙin juyayi ƙarƙashin jagorancin Malam Nasiru Fudiyya Kano, mahalarta taron sun saurari jawabin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) wanda ya yi bayani kan abubuwan da suka faru a rana ta uku ga watan Muharram. Hakazalika, an kammala zaman da karatun Ziyarar Ashura, inda aka sanar da cewa za a ci gaba da zaman domin gudanar da taron Ranar Jaririn Imam Husain (AS), Abdullahi Radee (Ali Asghar).
Gudanar da waɗannan taruka kowace shekara cikin tsari a Najeriya, hujjace bayyananna da ke nuna yadda saƙon Ashura ya shiga cikin zukatan al'umma 'yantattu na duniya, kuma yana tabbatar da cewa ruhin jihadi, basira, da neman adalci yana raye a tsakanin Musulmin Afirka.
















Ra'ayinka